Sunday, 20 January 2019

GWAGWARMAYAR JANYO TEKU RUWA ZUWA AREWA

Aikin janyo tashar jiragen ruwa zuwa Arewa ya fara ne a lokacin tsohon Shgaban Kasa, Marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’adua, wanda gwamnatin sa ta fitar da makudan kudade domin aiwatar da aikin tashar jirgin ruwa ta Baro Port a jihar Niger. Sai dai aikin ya gamu da tafiyar hawainiya a lokacin da Shugaban ya fara jinya. 


Bayan rasuwar Shugaban Kasa Yar’adua, Shugaba Jonathan da ya gaje shi ya umurci ma'aikatar kudi ta maido da kudaden aikin tashar Jiragen Ruwa wadanda suka kai Naira Biliyan 19 zuwa asusun ma'aikatar Raya Yankin Neja-Delta domin yin wani muhimmin aiki a yankin na Neja-Delta. Daga wannan lokaci murnar da 'yan Arewa ke yi na samun babbar tashar Jiragen Ruwa ta farko a yankin ta koma ciki.

Daga zuwan Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 ya bada umarnin bincike kan abun da ya haifar da tsayawar aikin, sannan daga bisani aka sake ware wasu makudan kudaden, aiki kuma ya ci gaba gadan- gadan, cikin ikon Allah a jiya tarihi ya kafu, inda Shugaba Buhari ya bude wannan Babbar Tasha ta Baro Port, kuma wanda ita ce tashar jirgin ruwa ta farko a yankin Arewa.

AMFANIN TASHAR JIRGIN RUWA GA YANKIN AREWA

• Tashar tana karamar hukumar Agaie dake jihar Neja

• Tashar za ta samar da guraben ayyuka da suka kai Miliyon Biyu.

• Sanadiyar tashar, manyan jiragen Ruwa masu dauko manyan kaya zasu fara shigowa Arewacin Najeriya.

• Dan Arewa zai samu saukin jigilar kayan da ya sayo daga kasashen waje.

 • Zamu huta da zuwa Tashar Jiragen Ruwa dake kudanci domin karbar kayan da muka sayo a kasashen ketare.

Wadannan sune kadan daga cikin amfanin da tashar Jiragen Ruwa ta Baro za ta kawowa yankin Arewacin Najeriya. 

Wannan na cikin namijin kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari yayi wa yankin Arewa wanda ba za a taba mantawa da shi ba.

Daga Haji Shehu Da Bashir Ahmad


No comments:

Post a Comment