Sunday, 6 January 2019

Gwamna Ganduje Zai yi Katafariyar Cibiyar Cutar Kansa Kan Kudi Naira Bilyan 2.5 A Kano

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kai ziyarar duba filin da Gwamnatin Jihar Kano za ta fara gina babbar Cibiyar cutar Cancer akan kudi naira biliyan biyu da rabi a babban asibitin koyarwa na Muhammadu Buhari dake Gigunyu don saukaka yadda mutane ke fita kasar waje saboda wannan cuta.


A tare da Gwamna akwai Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas, dan takarar majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi Engr Abubakar Kabir Bichi da kuma shugaban hukumar kula da Asibitoci Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa.

Daga Abubakar Aminu Ibrahim 
SSA Social Media II,Kano.


No comments:

Post a Comment