Friday, 11 January 2019

Gwamna Yari Na Jihar Zamfara Ya Yi Wa Shugaban Izala Sheik Sani Yahaya Jingir Kyautar Motoci Kirar Jeep

Shehk Abdullahi Umar Dalla Dalla tare da mataimakan shi ustaz Umar Hassan da sakataren shi Dinawa da wakilin gwamnatin jihar zamfara sun gabatar wa da Shehk Muhammad Sani Yahaya Jingir shugaban malamai na kasa da kasa tare da mataimakin shi Shehk Yusuf Sambo Rigacukum sabbin motoci kirar jeep dan su cigaba da yada sunnah da karartaswa burane da kauyuka dan Al'umar musulmai su gane addini.


Saidai an kai ruwa rana da Shehk Jingir kafin ya karbi motor kuma wakilan nan sai da suka yi bayanai masu kama hankali da kuma karin neman addu'a dangane da halin da jihar take ciki.

Bayan Sheik Jingir ya karbi motocin da kyar, nan take shi ma ya dauki tashi da yake hawa yabawa shugaba malamai na jihar Zamfara Shehk Abdullahi Umar Dalla Dalla da kudin mai dubu dari biyu.
Rariya.


No comments:

Post a Comment