Saturday, 5 January 2019

Gwamnatin Buhari zata kama Obasanjo idan..

Shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana cewa akwai yiyuwar gwamnatin shugaban kasa, Muhammdu Buhari ta gurfanar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo gaban kuliya akan kudin da aka kashe a harkar wutar Lantarki.


Oshiomhole yayi wannan maganne a jihar Flato inda ya kaddamar da yakin neman zaben gwamnan jihar, Simon Lalong, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa a shekarar 1999 Obasanjo da Atiku lokacin suna yakin neman zabe sun yi alkawarin cewa idan aka zabesu zasu gyara wutar lantarki cikin watanni shida. Amma bayan zabensu sai ma rashin wutar karuwa yayi.

Ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Obasanjo ta kashe dala biliyan 16 akan gyaran wutar amma ba'a gani a kasa ba, yace lokacin da Buhari yazo a shekarar 2015 ya tambayi ina wutar take? Yace to idan fa Buharin zai ci gaba da waccan tambayar tashi har zuwa karshe to dole fa a kamo Obasanjo.

Ya kuma gargadi 'yan Najeriya cewa Atiku da Obi manufar Obasanjo ce zasu ci gaba da yadawa domin gashi har Atikun yayi alkawarin saida kamfanin mai na kasa, NNPC to idan dai yaci zabe gaba dayan Najriyar ma zai iya saidata dan haka kada a zabesu.

No comments:

Post a Comment