Thursday, 3 January 2019

Hoton A'isha Buhari ta yi alamar 4+4 ya dauki hankula

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari kenan a wannan hoton nata da ya dauki hankula sosai, ta saka hotonne inda ta daga hannuwa sama da yatsu hudu, watau alamar 4+4 kenan dake bayyana sake zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zaben 2019.A'isha ta yi wannan abune a wajan kaddamar da tawagar yakin neman zabe ta mata da matasa da ta shiryawa mijin nata yau a Abuja.

Wannan alama dai ta 4+4 an fara yintane a jihar Kano yayin da masoyan gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje suka mai yayin wani gangami.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ma yayi wanan lama yayin da yaje gabatar da kasafin kudin 2019 a majalisar tarayya.

No comments:

Post a Comment