Wednesday, 23 January 2019

Hotunan batsa dana gani a wayarshi suka hada mu fada>>Inji Maryam Sanda matar da ake zargi da kashe mijinta

Matarnan da ake zargi da kashe mijinta a shekarar 2017 da ta gabata, Maryam Sanda ta bayyanawa kotu cewa dalilin fadan da ta yi da mijin nata, Bilyaminu Bello ta ga hotunan batsa na wata mata ne data turomai.A lokacin sauraren karar da aka yi jiya, Talata 'yar sandar dake bincike akan lamarin ta shaidawa kotu cewa Maryam a cikin bayanin data bata tace hoton batsa na wata mata da ta gani a wayar mijinta shine ya jawo fadan da suka yi.

Data fuskanceshi da maganar suna cikin fada sai ya fadi kasa kan fasasshiyar kwalbar shisha wadda tasa ya ji rauni sosai, Maryam ta kara da cewa ta dauki mijin nata zuwa Asibiti inda acanne likita ya tabbatar da cewa ya mutu.

Lauyan dake kare Maryam yayi kokarin bayar da sakamakon binciken da likita yayi akan gawar marigayi bilyaminu amma lauyan wanda ke kara yace be yadda ba saidai likitan da yayi wannan bincike da kanshi ya zo ya gabatar da wannan sakamako.

An daga karar zuwa watan fabrairu.

No comments:

Post a Comment