Monday, 7 January 2019

Hukumar 'yansanda sunce Dino Melaye ya samu sauki sosai yanda zai iya tsayuwa a gaban shari'a

Hukumar 'yansanda ta tabbatar da cewa Sanata Dino Melaye ya samu sauki sosai daga rashin lafiyar da ta kamashi yayin da jami'an tsaro suka je gidanshi kamashi bisa zargin hannu da yake dashi a yunkurin kisan jami'in dansanda.Mataimakin shugaban 'yansanda Mr Kaomi Ahmadu ya bayyanawa manema labarai cewa yanzu Dino Melaye ya samu sauki sosai ta yanda zai iya tsayuwa a gaban shari'a, kamar yanda Dailypost ta ruwaito.

Ya kara da cewa duk da Dinon ya bayyana musu cewa yana bukatar karin kulawa amma zasu yi kokarin ganin an bashi duk kulawar da ta kamata.

No comments:

Post a Comment