Friday, 11 January 2019

Idan Atiku ya ci zabe zai maida hankaline wajan azurta kanshi da abokanshi>>Inji rahoton kasar Amurka

Wata kungiya me zaman kanta a kasar AMurka Eurasia dake sa ido akan harkokin siyasar Duniya ta bayyana cewa idan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya lashe zaben 2019 to zai azurta kanshine da abokanshi.Eurasia ta kara da cewa amma duk da haka Atikun zai fi yin katabus akan shugaban kasa, Muhammadu Buhari saboda ya fi Buharin lafiya da sanayyar tattalin arziki. Eurasia tace Atikun zai dan farfado da harkar tattalin arziki na dan lokaci sannan kuma zai amshi bashin kudi sosai daga kasashen waje.

Eurasia ta bayyana hakane a cikin rahoton da ta fitar na shekarar 2019 wanda ta saba fitarwa duk shekara, kamar yanda Guardian ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment