Friday, 4 January 2019

Idan kuka duba kokarin da gwamnatina ta yi cikin shekaru 3 da rabi ba zaku yi dana sanin sake zabena ba>>Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya roki kungiyoyin kwadago, musamman kungiyar malaman jami'a dake yajin aikin da su bar gwamnatinshi ta sarara dan ta samu farfado da matsalolin ababan more rayuwa ga 'yan Najeriya.Yayi wannan kirane a lokacin da ya gana da kungiyar dalibai ta kasa, inda yace cikin shekaru 3 da rabi da suka yi suna mulki sun yi kokari sosai wajan farfado da ababen more rayuwa da suka iske.

Me magana da yawunshi Femi Adesina ya ruwaitoshi yana cewa, ko daga wane bangare na kasarnan ka fito zaka ga alamar kokarin da muke na gyara tituna da wutar lantarki, titunan jirgin kasa dadai sauransu kuma idan ka duba kokarin da muka yi a cikin shekaru 3 da rabi ba zaka yi tantamar sake zaben mu ba.

Buharin yayi alkawarin yiwa kungiyar ta malaman jami'a magana dan su janye yajin aikin da suke saboda kar su tsawaitawa daliban lokacin kammala makaransu.

No comments:

Post a Comment