Wednesday, 9 January 2019

Idan kuka samu matata, A'isha ko dana Yusuf da samun kudi ta hanyar da bata dace ba ku fallasa>>Shugaba Buhari ya gayawa 'yan jarida

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kalubalanci 'yan jarida da su bincika su gano, idan kwai inda iyalinshi suka aikata ba daidai ba na samun kudi da harkar gwamnati su kuma yada.Shugaban ya bayyana hakane a hirar da yayi da Arise TV, inda yace zargin da ake cewa ana wa iyalanshi na amfani da matsayin da yake dashi wajan samun kudi cin fuskane gareshi, yace yana kalubalantar 'yan jarida da su bincika idan suka samu matarshi, A'isha ko kuma danshi Yusuf da amfani da matsayinshi wajan azurta kansu daga wasu ma'aikatun gwamnati to su watsawa Duniya ta ji.

Akan maganar tsohon gwamnan Akwa-Ibom, Godswill Akpabio kuwa an tambayi shugaba Buhari me zai ce akan zargin da ake na cewa bayan da ya koma APC shugaban ya buka ci da a tsayar da binciken badakalar sama da fadi da naira biliyan 100 da ake maI

Buhari yace, be taba gayawa EFCC ko ICPC ko 'yansanda ko kuka wata hukuma su bar Akpabio ko kuma wani da suke bincika ba idan kuma an samu hakan to a gayawa Duniya.

Shugaban ya kuma ce be yadda da cewa akwai matasa miliyan 20 a kasarnan da basu da aikin yi ba.

No comments:

Post a Comment