Friday, 4 January 2019

Idan Yari ba zai iya ba ya yi murabus kawai, amma ba za mu amince a saka dokar ta baci ba a Zamfara>>Atiku

Dan Takarar shugaban Kasa a inuwar Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya soki kiran da gwamnan jihar Zamfara ya ke yi na a saka dokar ta baci a jihar saboda rashin tsaro da ake fama da shi.


A takarda da Pharank Shuaibu ya fitar a madadin Atiku, ya ce wannan shiri ne kawai don a muzguna wa ‘Yan siyasa.

” Idan gwamnan jihar Yari ba zai iya ba kaucewa zai yi ya ba da wuri amma ba wai ya rika kira da a saka dokar ko ta baci a jihar ba. Yin haka sabawa doka ce da kuma muzguna wa mutane. Ana neman yadda za a takura wa mutane ne kawai a hana su walwala saboda son zuciya da kuma dagewa da Buhari yayi na sai dole-dole ya zarce ko da karfin tsiya ne.

Atiku ya kara da cewa muddun aka yi haka za a saka shingaye a tituna da wurare da dama a jihar da hakan zai takura wa walwalar mutane.
Premiumtimeshausa.

No comments:

Post a Comment