Sunday, 6 January 2019

Itacen girki na karanci a Maiduguri



A garin Maiduguri babban birnin jihar Borno, da ke arewa-maso-gabashin Najeriya jama'a na kokawa game da karancin itacen girki da kuma gawayi.

To ko me ya jawo hakan?
Wani mutum da ya dogara da sana'ar shigo da itacen girki da gawayi daga wasu jahohin na Najeriya ya ce jami'an tsaro kan hana motoci masu dauke da itacen ko kuma gawayi shiga birnin na Maiduguri.

A cewarsa 'Amma na ji an ce an dauki wannan mataki ne saboda tsaro.'

Ya kuma kara da cewa a yanzu itacen girki da ake sayarwa Naira 250 ya kara farashi zuwa Naira 300.

Jihar Borno dai ita ce a tsakiyar matsalar tsaro na rikicin Boko Haram, wanda aka kwashe sama da shekara 10 ana fama da shi.

A kwanakin baya, mayakan Boko Haram sun rinka amfani da daidaikun mutane ko yara mata wajen kai harin kunar-bakin-wake kan al'umma a birnin Maiduguri.

A baya-bayan nan kuma mayakan sun tsananta kai hare-hare kan sojojin Najeriya, gabanin babban zaben kasar na shekarar 2019.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment