Sunday, 13 January 2019

"Iya kibarka iya kankantar kwakwalwarka"

Wasu kwararrun masana a fannin kwakwalwa na nahiyar Turai sun gano cewa kwakwalen masu kiba 'yar kankanuwa ce,kuma tana ci gaba da rage girma a duk lokacin da jikin mutum ya kara nauyi.


Masanan sun dai wallafa sakamakon wani zurfaffen bincike da suka yi a mujjalar kiwon lafiya ta Neurology.

Kwararrun dai sun gudanar da gwaje-gwaje kan akalla mutane dubu 9,600 wadanda suka gabatar da kawunansu a gare su a matsayin zakarun gwajin dafi.Yawancin wadannan mutanen na da shekaru 55 zuwa sama kana kashi 19 cikin dari masu kiba ne.

A tashin farko,masanan sun auna nauyin jiki, fadin cinya da kuma tsayin kowane mutum,inda daga bisani suka auna girma yawan fararen sinadaren da ke cikin kwakwalwar kowane daga cikin ta hanyar amfani da fasahar MRI.

Mutanen da aka yi wa wadannan gwaje-gwajen sun bada cikakkun bayanai ta'ammalinsu da taba-sigari,motsa j,ki karfin gudanuwar jini a jiyoyin jikinsu da kuma shekarunsu na haifuwa.

An gano cewa dukannin wadanda kibar jikinsu ta wuce iyaka, kwakwalwarsu 'yar kankanuwa ce duba da ta 'yan lenge-lenge wadanda ke motsa jiki lokaci zuwa lokaci.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment