Sunday, 6 January 2019

Ka jawa matarka kunne ta daina magana akan gashina duk inda taje ko kuma in kai kararta gurin malamai>>Shehu Sani ya gayawa gwamna

Sanata me wakiltar Kaduna ta tsakiya,Shehu Sani ya gargadi wata matar gwamna da yace duk inda taje tana ta magana akan gashin shi, Shehu Sani dai be kira suna ba amma ya ce gwamnan ya jawa matarshi kunne.A wani sako da ya fitar ta dandalinshi na Twitter yace yana jawo hankalin gwamna da ya jawa matarshi kunne akan yawan maganar gashinshi da take a duk inda take yin yakin neman zabe, yace shi fa ba laifinshi bane mijinta bashi da gashi, yace yana kallon wannan magana a matsayin kalaman kiyayya idan ba ta daina ba zai kai kararta gurin Dr. Gumi ko kuma majalisar malamai. Shehu Sani ya kare rubutunshi da cewa haba jama'a.

Sanata Shehu Sani dai da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai sun jima basa ga maciji inda na hannun damar gwamna  ya fito neman takarar kujerar Shehu Sanin dalilin haka Shehu Sani be samu tikitin tsayawa takarar kujerar da yake kai a jam'iyyar APC ba, ya canja jam'iyyar zuwa PRP.

No comments:

Post a Comment