Thursday, 3 January 2019

Ka yadda ka sha kasa Ka fito ka goyamin baya kawai>>Buhari ya gayawa Atiku

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ta hannun me magana da yawun kungiyar yakin neman zabenshi, Festus Keyamo ya bukaci dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019,Atiku Abubakar da ya dawo ya goyamai baya maimakon kirkirar karya yana jingina mai.Festus Keyamo ya mayar da martanine akan maganar da Atikun yayi ta cewa iyalan Buhari na da hannun jari a cikin kamfanonin bankin Keystone da kamfanin sadarwar Etisalat. Festus Keyamo yace tunda yanzu kamfanonin sun fito sun karyata wannan zargi sai Atiku ta fito ya baiwa 'yan Najeriya da iyalin Buhari hakuri ya kume nemi gafarar su kamar yanda Dailytrust ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment