Tuesday, 8 January 2019

Kalli dandazon taron da akawa Atiku a jihar Kogi

Wadannan hotunan taron da jama'a suka wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar kenan a jihar Kogi inda yaje yakin neman zabe Jiya, Litinin.Atiku ya bayyana cewa, shi da kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki tare da sauran wasu 'yan Najeriya a shekarar 2015 sun yi kiskuren zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari amma basu ga ribar zaben nashi ba.

Atiku ya bayyana cewa abinda ya fi mayar da hankali akai shine canja fasalin kasa kuma jihar Kogi na daga cikin jihohin da zasu fi moriyar canja fasalin kasarnan dan haka su yi kokarin zabar shi a zabe me zuwa.

Shima Bukola Saraki yayi maganar kama sanata Dino Melaye dake hannun 'yansanda inda yace matashin dan siyasane me hazaka kuma sun bukaci da a sakeshi.No comments:

Post a Comment