Wednesday, 23 January 2019

Kalli karin kayatattun hotuna daga gurin yakin neman zaben Shugaba Buhari a Sakkwato

Karin kayatattun hotunan shugaban kasa, Muhammadu Buhari na yakin neman zaben da yaje yi jihar Sakkawato kenan inda dubban masoyanshi suka mai taro na ban mamaki.Ga kalaman Buhari a gurin yakin neman zaben:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta cigaba da mayar da hankali a kudurorin yaki da cin hanci da rashawa, tsaro da kuma bangaren aikin gona domin samar da ayukkan yi ga 'yan kasa.

Shugaban ya bayyana hakan ne, yayin yekuwar neman zaben sa da ya gudanar a jihar Sakkwato.

Ya ce dukkanin cigaban kowace kasa, ya rataya ne bisa tattalin arziki, kuma hakan zai samu ne ta hanyar habaka bangaren aikin gona.

Kuma daga sama har kasa APC sak inji shi.

Shi ma da yake tsokaci, ministan sufuri Rotimi Amechi, ya ce ma'aikatar sa za ta samar da layin dogo daga Jibiya ta jihar Katsina da zai sada jihohin, Zamfara, Sokoto da jihar Kebbi, domin habaka bangaren kasuwanci a kasar nan.


No comments:

Post a Comment