Tuesday, 1 January 2019

Kalli Mace da namiji da suka fi kowa kyau a Duniya a shekarar 2018

Wannan itace matashiyar da tafi kowace mace kyau a Duniya a shekarar 2018 data gabata kamar yanda masu tattantance kyawawan mutane na TC Chandler suka bayyana.'Yar kasar Faransa me suna Thylane Blondeau wannan ne karo na biyu da take lashe wannan kyauta, tun tana 'yar shekaru 7 a Duniya a shekarar 2007 ta taba lashe wannan kyautar a matsayin karamar yarinyar da ta fi kowace karamar yarin kyau.
Gashi yanzu shekaru goma bayannan ta kara lashe kyautar a matsayin matashiyar da tafi kowace kyau.

Bayan wannan matashiya akwai kuma namijin da ya fi kowane kyau a wannan shekarar.
Sai kuma tauraron fina-finan kasar Amurka, Jason Momoa wanda shine yazo na daya a cikin mazan da suka fi kyau a Duniya.
Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ne yazo na 72.
Sai kuma tauraron dan kwallon kasar Argentina me bugawa kungiyar Barcelona, Lionel Messi da yazo na 98.

No comments:

Post a Comment