Sunday, 13 January 2019

Kalli wadda ta kirkiro inkiyar 4+4

 Inkiyar shugaban kasa, Muhammadu Buhari a neman sake zabenshi a zabe me zuwa itace 4+4 wadda masoyanshi ke daga hannaye sama da nuna yatsu hudu, da dama an amince cewa daga birnin Kano ne wannan inkiya ta samo asali, saidai ko wanene ya kirkirota? Me baiwa gwamnan Kano shawara ta fannin kafafen watsa labarai na zamani, Salihu Tanko Yakasai yace wannan matarce.Salihu ya rubuta cewa, kasancewar inkiyar 4+4 ta zagaye Duniya, bari in gabatar muku da matar da ta kitkiri wannan inkiya a Kano a matsayin inkiyar gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Itace Hajiya Sa'adatu Babaji, tsohuwar shugabar gidan rediyon Kano wadda kuma a yanzu itace me baiwa gwamnan Kanon shawara ta musamman akan harkokin mata.


No comments:

Post a Comment