Monday, 7 January 2019

Karanta abinda Amaechi yace akan maganar da akace yayi akan shugaba Buhari

Shugaban tawagar yakin neman zaben shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya fito yayi magana akan muryar dake ta yawo tsakanin 'yan Najeriya wadda akace tashi ce inda aka jishi yana sukar gwamnatin shugaban kasa,Muhammadu Buhari da cewa baya sauraren shawara kuma be damu da abinda mutane ke cewa a kanshi ba.Jaridar Sun ta ruwaito cewa, Amaechi ya karyata wannan labari inda yace shi be san da wata muryarshi da aka nada ba.

Wannan dai ya jawo ece-kuce sosai musamman tsakanin ma'abota amfani da shafikan yanar gizo.

No comments:

Post a Comment