Sunday, 13 January 2019

Karanta labarin yanda wata baiwar Allah ta samu tsaida da sallah

Wata baiwar Allah ta bayar da labarin yanda ta yi fama da kokarin tsayar da Sallah shekaru 4 da suka gabata, tace ta fara da yin sallah daya a rana, watau Sallar Subahi.


Ta kara da cewa a haka a haka, wani lokacin ta yi akan lokaci wani lokacin kuma tayi bayan lokaci har ta samu yanzu tana tsayar da salloli 5 a rana.

Ta kara da cewa tana baiwa wanda ke fama da tsayar da sallah shawara da ya fara da kadan-kadan wataran zai samu tsayar da sallah biyar.

Ta karkare da cewa Allah ya sauwaka mana damar tsayar da salloli 5 a rana.


No comments:

Post a Comment