Wednesday, 9 January 2019

Khadija Bukar Abba Ta Yi Murabus Daga Mukamninta Na Minista

Uwargidan tsohon gwamnan jihar Yobe Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim ta yi murabus daga kujerarta na karamar ministan harkokin kasashen waje na Nijeriya. 


Jaridar Punch ta ruwaito cewar, Hajiya Khadija ta yi murabus ne domin shiga zaben majalisar wakilai da za a gudanar ranar 16 ga watan Feburairun 2019 a karkashin tutar jam'iyyar APC.

Daga Haji Shehu


No comments:

Post a Comment