Monday, 14 January 2019

Kotu ta bayar da damar sauraren karar dake bukatar kama da hukunta matar gwamnan Kano bisa hannu da ake zarginta dashi a cikin badakalar dala miliyan 5 ta mijinta

Babbar kotu dake zaune a babban hirnin tarayya, Abuja ta bada damar sauraren karar dake bukatar a gurfanar da matar gwamnan jihar Kano, Dr. Hafsat Umar Abdullahi Ganduje dan hukuntata bisa hannu da ake zarginta dashi a badakalar dala miliyan 5 da mijinta ke ciki.
Alkali Yusuf Halilu ya bukaci jam'iyyar APC, gwamnatin jihar Kano da hukumar EFCC da su bada kwararan hujjojin da zasu hana dakatar da amfani da kadarorin gwamna Ganduje da matarshi Hafsat harsai an kammala sauraren karar dake gaban kotun.

Haka kuma alkalin ya bukaci jam'iyyar APC ta bashi dalilai da zasu hana kotun tasa su canja sunan gwamna Ganduje a matsayin dan takarar gwamnan jihar ta Kano.

Masu shigar da karar ne dake karkashin Incorporated Trustees of Hope Development and Empowerment Foundation suka bukaci da kotun ta dakatar da gwamnan da matarshi amfani da kadarorinsu har sai an kammala sauraren shari'a.

Amma alkalin be bayar da wannan dama ba inda ya bukaci wadanda ake kara da su bayyana a gaban kotu ranar 31 ga watan Janairu dan bashi dalilin da zai hanashi bayar da waccan oda, Kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment