Wednesday, 23 January 2019

Kuci gaba da noma kada ku gajiya>>Shugaba Buhari ya gayawa 'yan Najeriya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba da baiwa gwamnatin tarayya goyon baya a kokarin da take na ganin ta canja akalar dogaro da man fetur wajan samun kudin shiga da kasarnan ke yi.
Shugaban yayi wannan kirane a jihar Kebbi yayin yakin neman zabenshi, inda yace a shekarar 2015 yayi yakin neman zabe akan abu 3, tattalin arziki, tsaro da yaki da rashawa da cin hanci.

Shugaban yace, jama'ar Borno sun tabbatar da ci gaba wajan samar da tsaro sannan shekaru biyu da suka gabata an samu yabanya me kyau ta yanda gwamnati ta yi maganin shigo da shinkafa da kashi 90 cikin dari. Yace yana fatan wannan shekarar ma a samu irin wancan sakamako inda yace aci gaba da noma kada a yi kasa a gwiwa.

No comments:

Post a Comment