Sunday, 13 January 2019

Kuskuren rubutu da Ali Nuhu yayi wajan yin murnar zagayowar ranar haihuwar diyarshi ya jawo cece-kuce

A yaune tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya taya diyarshi, Fatima murnar zagayowar ranar haihuwarta, saidai a dandalin sada zumunta na Facebook kuskuren da Alin yayi wajan rubutu ya dauki hankulan wasu daga cikin masoyanshi.


Alin ya rubuta cewa, ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwarki sarauniyata, Fatima Ali Nuhu, Allah ya miki Albarkan ya kuma shiryar dake (ba) hanya madaudaiciya ba.

Wancan kuskure da Alin yayi ya dauki hankulan wasu daga cikin masoyanshi inda suka rika jawo hankalinshi akai yayin da wasu ke ganin hakan ba komai bane dan babu wanda ya fi karfin yin kuskure.

No comments:

Post a Comment