Saturday, 12 January 2019

Liverpool ta bada tazarar maki 7 a saman teburin Frimiya da kyar

Kwallon da Mohamed Salah yaci daga bugun daga kai sai golace ta tseratar da Liverpool da kyaar a hannun Brighton a wasan da suka buga yau wanda a haka aka tashi wasan Liverpool na cin 1-0.Duk da cewa Liverpool dince ta mamaye filin wasan da wasa mafi kayatarwa da nuna kwarewa amma masu sharhi na ganin bata yi abinda ta saba yi ba ko kuma ake tsammani.
Yanzu dai Liverpool din ta bayar da karin tazarar maki 7 a saman teburin na Firmiya.

No comments:

Post a Comment