Monday, 7 January 2019

Madrid ta koma ta biyar a teburin La Liga bayan da ta sha kashi a hannun Real Sociedad da ci 2-0

Real Madrid ta ci karo da koma baya a kokarin lashe kofin La Liga na bana, bayan da Real Sociedad ta doke ta 2-0 a Santiago Bernabeu.


Willian Jose ne ya fara ci wa Sociedad kwallo a bugun fenarity a minti uku da fara wasa, bayan da dan kwallon Real, Casemiro ya yi wa Mikel Merino keta a cikin da'ira ta 18.

Wasan ya kara sa Madrid a matsi bayan da aka bai wa Lucas Vazquez jan kati, bayan da aka koma wasa daga hutun da suka yi.

Daga baya ne Sociedad ta kara kwallo na biyu ta hannun Ruben Pedro daf da za a tashi daga karawar.

Rashin nasarar da Madrid ta yi ya sa ta yi kasa zuwa mataki na biyar da maki 30, kuma karon farko da Sociedad ta yi nasara a gidan Real tun bayan shekara 15.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment