Thursday, 24 January 2019

Mahaifiyar Ahmed Musa ta rasu

Tauraron dan kwallon Najeriya dake bugawa kungiyar Alnassr ta kasar Saudiyya wasa, Ahmed Musa ya yi rashin mahaifiyarshi, Ahmed Musa ya bayyana hakane a dandalinshi na sada zumunta.Ahmed Musa ya bayyana cewa, yauce rana mafi muni a rayuwata, na yi rashin mahaifiyata.

Dama dai kamin hakan Ahmed Musa ya saka wata Addu'ar neman sauki da yakewa mahaifiyar tashi da bata da lafiya.

Muna fatan Allah ya bashi da sauran 'yan uwa hakurin rashi ya kyautata makwancinta.

No comments:

Post a Comment