Monday, 7 January 2019

Malaman kasar Tunisia sun yi zanga-zanga kan daidaita gadon maza da mata

Manyan Limamai a kasar Tunisia sun gudanar da zanga-zanga inda sunka yi kira da kar a sake zaban shugaban kasar Beji Caid Essebsi a zabukan dake tafe in har ya amince ya kuma rataba hannu akan dokar da zata dai-daita gadon mace dana namiji a kasar.


Kungiyar Malamai ta kasa a Tunisia ta gudanar da zanga-zangar kalubalantar shirin dai-daita gadon mace dana namiji a lokacin da mambobin kungiyar sunka taru a gaban wani katabare ginar gwamnati a babban birnin kasar Tunis.

Bayan gudanar da zanga-zanagar kungiyar Limaman kasar ta fitar da sanarwa a rubuce inda ta yi kira ga dinbin al'ummar kasar da karsu zabi shugaba Essebsi da dukkan wadanda sunka bayar da goyon baya ga dokar dai-daita gadon maza da mata tun daga shugaban kansa har izuwa jam'iyyu da sauran 'yan siyasa a kasar, duk wanda ya goyi bayan wannan tsarin da ya sabawa addini ba za'a zabe shi a zaben dake tafe gaba ba a kasar.

Shugaban kungiyar Limaman kasar Tunisiya Muhammed Salih Redid ya bayyana cewar muna gudanar da wannan zanga-zangar ne domin mu nuna matsayarmu akan kalubalantar yunkurin gwamnati na dai-daita gadon maza da mata. Muna mai kuma tsayuwa tare da goyon baya ga Limaman da sunka tsare hukunci da dokokin Al'Qur'ani mai girma. Zamu ci gaba da kalubalantar wannan tsarin da ya sabawa addininmu da al'adunmu, inji kungiyar Malamai a kasar ta Tunisiya.

Redid, ya tabbatar da cewa wannan sabuwar dokar ba wai dokar littafin Allah madaukaki sarki da sunnan Manzo kawai ya sabawa ba, ya kuma sabawa al'adun kasar baki daya.

Shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi a jawabin da ya yi a taron matalisar zartarwar kasar a ranar 23 ga watan Nuwamba  ya bayyana amincewarsa  akan kudirin dai-daita gadon mace da na miji a kasar.

Bayan gwamnatin kasar ta amice da shi ana jiran a aika da dokar a gaban majalisa, bayan dokar ta samu amincewar majalisa zata kaita akan teburin shugaban kasa domin rataba mata hannu.


A kasar Tunisiya dai dake da dinbim malamai da Musulmi wannan dokar ko shakka babu zata ci gaba da haifar da ka-ce-na-ce a kasar.  
TRThausa.


No comments:

Post a Comment