Thursday, 10 January 2019

Man City ta casa Burton da ci 9-0

Kafar Manchester City daya ta kai wasan karshe a gasar Caraboa Cup, bayan da ta casa Burton Albion da ci 9-0 a karawar da suka yi a Ettihad a ranar Laraba.


City ta ci kwallayen tara ta hannun De Bruyne da Zinchenko da Foden da Walker da Mahrez da Gabriel Jesus wanda ya ci hudu a karawar.

Manchester City za ta ziyarci Burton a wasa na biyu a ranar 22 ga watan Janairu.

A ranar Talata ne Tottenham ta ci Chelsea daya mai ban haushi a daya wasan daf da karshe a gasar ta Caraboa Cup ta bana.

Manchester City ce ke rike da Caraboa wanda ta doke Arsenal da ci 3-0 a kakar 2017/18.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment