Wednesday, 9 January 2019

Masar ta samu sukunin karbar bakoncin gasar cin kofin Afrika ta 2019

Kasar Masar ta samu zarafin karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika da za ta fara gudana cikin watan Yunin shekarar nan, bayan taron da ya gudana yau tsakan-kanin shugaban hukumar CAF can a birnin Dakar na Senegal.

A cewar shugaban hukumar Ahmad Ahmad CAF ta gamsu da matakan daukar nauyin gasar na Masar fiye da shirye-shiryen Afrika ta kudu, sai dai y ace duk da haka yana godiya ga Afrika ta kudun da ta yi rashin nasara da kuma Masar wadanda suka nuna sha’awar karbar bakoncin gasar bayan matsalar da suka fuskanta a Kamaru.

Rahotanni sun ce yayin kada kuri’ar da mambobin hukumar suka yi da safiyar yau kan kasar da za ta karbi bakoncin, Masar ta samu kuri’u 16 yayinda Afrika ta kudu ta samu kuri’a 1 sai kuma jami’I guda da ya kauracewa zaman.

Wannan ne karo na 5 da Masar ke neman karbar bakoncin gasar ta na rasawa tun bayan 1959 lokacin da kasar ta kira kanta Jamhuriyyar Larabawa, haka zalika ta nema a shekarun 1974 da 1986 da kuma 2006 amma duka ta na rasawa, sai kuma a wannan karon bayan kubcewar damar daga Kamaru.

Haka zalika shekaru 13 kenan rabon da gasar ta shiga hannun wata kasa da ke yankin Arewacin Afrika.

Rahotanni na nuni da cewa lokacin gasar zai kasance a tsakiyar zafi yayinda kasar ta sha alwashin daukar matakan tsaro sakamakon hare-haren ta’addancin da ta ke fuskanta a wasu sassanta.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment