Sunday, 6 January 2019

Matan Saudiyya za su fara samun sakon saki ta wayar salula

Wata sabuwar dokar kasar Saudiyya za ta baiwa mata damar sani idan mazajensu sun sake su, ba kamar yadda a da iyaye ko muharammi ne ke fara sani ba.


Daga ranar Lahadi kotunan kasar za su bukaci mazan aure su aika wa matansu shaidar saki ta hanyar sakon wayar salula.

Wannan mataki ya zo da ban mamaki a daidai lokacin da ake ta muhawara kan bai wa mata 'yancin tuka mota a kasar ta Saudiyya da ke bin tsarin addinin musulunci.


Ana kuma ganin wannan matakin zai kara yawan mace-macen aure a kasar.

Amma hukumomi sun ce mata da yawa sun shigar da kara a kotunan kasar kan mazajen na sakinsu ba tare da saninsu ba.

Don haka ana ganin yawanci mata ba su san takamaimai saki nawa mazan kan musu ba har sai idan auren ya kare baki daya sai iyaye su ce matar ta tattaro kayanta ta koma gida.

Watakila kuma ita saki daya kadai ta san an taba yi ma ta.

Kawo yanzu malaman addinin musulunci ba su ce komai ba, ban da 'yan kasa da ke bayyana ra'ayoyi mabanbanta.

To amma lauyoyi mata sun yi marhabin da matakin inda suke cewa a ganinsu hakan zai magance matsalar da ke faruwa ta maza kan saki matansu ba tare da saninsu ba.

Wasu lauyoyi biyu, Nasreen al-Ghamdi da Samia al-Hindi sun shaidawa jaridar Okaz cewa a yawancin lokuta mazajen kan fadawa iyaye ko muharramansu ne, kuma a wasu lokutan ma ba sa fada.

Sannan suna ganin matakin zai bai wa mata damar neman hakkinsu, misali idan namaji ya saki matarsa zai bata wani kaso cikin dukiyarsa wato "alimony" a turance.

Saboda rage radadin sakin auren, ko a iya cewa wata diyya da za ta sanyaya zuciyar macen da aka saki duk da cewa shi sakin aure ta kowacce fuska aka yi shi ba abu ne da za a ce mai dadi ba.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment