Thursday, 10 January 2019

Me goyon bayan Buhari ya soki Atiku akan wadannan hotunan, Dan Atikun ya mayar da martani

Wadannan hotunan na dan takarar shugaban kasa,Atiku Abubakar da matarshi sun yi ta yawo a shafukan sada zumunta inda jama'a suka ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai, wani me goyon bayan gwamnatin Buhari, Kayode Ogundaminisi yace, da Buhari ne a wadannan hotunan da kaji ana cewa gashican yana holewa da shugabar matan PDP a jihar Adamawa.Yace amma su ba zasu fadi haka ba saboda sun san Gaisawace kawai Atikun yake da ita.

Bayan wannan rubutu da Kayode yayi sai aka yi sa'a dan Atikun me suna Alhaji Mustafa ya gani ya kuma mayar masa da martani.

Ya rubuta cewa, mutumin dake wannan hoton mahaifinane, sannan kyakkyawar matar da yake nunawa soyayya kuma mahaifiyatace, wannan abu da kake yi be kamata ba, zaka iya nuna mishi duk irin kiyayyar da kake so wannan babu wanda zai zarge ka mama ita bai kamata ka mata haka ba. Dan Allah ka girmamata a matsayin mace sannan su gaba daya a matsayin ma'aurata.

No comments:

Post a Comment