Tuesday, 15 January 2019

Me goyon bayan Buhari yayi alkawarin sassauta sukar da yakewa Atiku saboda hidimar da Atikun kewa addinin musulunci

Wani bawan Allah ya ce min ko a yanzu kazo Yola duk ranar juma'a zakaji gidan Rediyo na Atiku Abubakar wato "Gotel Radio" suna suka karatun Sheikh Abdullahi Bala Lau na tsawon awa daya (1hr) daga karfe 9:00am zuwa 10:00am na safe, kuma a kyauta ake saka karatun ko sisi ba'a biya


Bayan wannan karatun na Sheikh Abdullahi Bala Lau da ake sakawa kyauta a gidan rediyon Atiku Abubakar akwai sauran malaman sunnah da suma ana saka karatunsu duk yawanci kuma kyauta ne

Idan watan Ramadan yazo gaba daya Atiku Abubakar yana rage kudin saka karatu da wa'azin Malamai a gidajen rediyo da talabijin mallakinshi, yana rage kudi kashi 50 cikin 100

Mutanen Yola ku bincika mana, indai ya tabbata Atiku Abubakar yana yiwa addinin Allah hidima haka, to wallahi ni Datti Assalafiy nayi alkawarin zan sassauto daga caccakar da nake mishi a babin siyasa insha Allah

Allah Ka biyashi da gidan Aljannah Amin
Datti Assalafiy.


No comments:

Post a Comment