Monday, 14 January 2019

Messi ya zama dan kwallo na farko da ya ci kwallaye 400 a La Liga

Lionel Messi ya ci kwallo 400 a gasar La Liga, bayan da Barcelona ta doke Eibar da ci 3-0 a gasar mako na 19 da suka kara a ranar Lahadi.


Luis Suarez ne ya ci sauran biyun da ya bai wa Barcelona damar samun maki biyar tsakaninta da ta biyu a teburin La Ligar bana.

Da wannan kwallon da Messi ya ci ya tsawaita tarihin cin kwallaye a gasar ta La Liga - Cristiano Ronaldo ne keda kwallaye fiye da 300 a fafatawa 435 da ya yi wa Real Madrid.

Messi wanda ya buga wa Barcelona wasa 22 a kakar 2018/19 ya ci kwallo 23, ciki har da 17 da ya zura a raga a gasar La Liga, kuma shi ne kan gaba a Spaniya.

Barcelona za ta karbi bakuncin Levante a wasa na biyu a Copa del Rey a ranar 17 ga watan Janairu, a wasan farko Levante ce ta yi nasara da ci 2-1.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment