Saturday, 5 January 2019

Miji ya bankawa kanshi wuta saboda matarshi da ta yi yaji taki yadda ta dawo

Hukumar 'yansanda na jihar Jigawa sun fitar da sanarwar cewa wani mutum me shekaru 40 ya bankawa kanshi wuta saboda matarshi da tayi yaji taki yadda ta dawo gidanshi.Hukunar 'yansandan ta hannun me magana da yawunta, SP Abdu Jinjiri ta bayyana cewa, ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2018 data gabata wata mata me suna Halima Abdullahi ta yi yaji daga gidan mijinta me suna Abdullahi Jafaru dan shekaru 40 dake kauyen Shunar a karamar hukumar Kafin Hausa.

Abdullahi yayi kokarin yaga sun daidaita da matar tashi da suke da 'ya'ya shida tare wadda kuma itace uwargidanshi amma hakan bata samu ba.

Ganin haka yasa Abdullahi yayi tunanin bazai iya rayuwa ba tare da matar tashi ba sai kawai ya samu fetur ya bakawa kanshi wuta.

Bayan 'yansandan yankin suka ji labari sai suka gaggauta zuwa gidan Abdullahi suka kaimai dauki inda suka garzaya dashi Asibiti.

Jinjiri yace koda Abdullahi ke kwance a gadon Asibiti ya ci gaba da kiran sunan uwargidanshi Halima dik da cewa amaryarshi na tare dashi, sannan ya kara da cewa suna kan bincike akan lamarin.

No comments:

Post a Comment