Friday, 11 January 2019

Mu yanzu mun tsarkaka dan kuwa duk barayin cikin mu sun koma APC>>PDP


Jam'iyyar hamayya ta PDP ta bayyana cewa yanzu ta tsarkaka da zargin mamaye ta da shuwagabanni da suka yi kaurin suna a cin rashawa da ake mata domin irin wadannan shuwagabanni duk yanzu sun koma APC.Wani dan majalisar tarayyane na PDP Kunle Okunola ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki a siyasa da wata kungiyar kiristoci ta shirya a birnin Legas, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Kunle Okunola ya kara da cewa yanzu duk shuwagabanni masu cin rashawa da PDP ke da su sun koma APC dan haka su yanzu sun tsarkaka, APC kuma ta koma uwar rashawa a Najeriya.

Ya kara da cewa su ne kadai jam'iyyar da ta yi amfani da tsarin dimokradiyya wajan nada shuwagabannin ta da kuma gudanar da zaben fidda dan takarar shugaban kasa, duk jam'iyyar da ta kasa samar da dimokradiyya a cikin tsarinta ta yaya zata iya warware matsalar Najeriya? Injishi.

No comments:

Post a Comment