Wednesday, 23 January 2019

Mun Zama Silar Arzikinka Kuma A Haka Za Ka Kare>>Martanin Yaran Atiku Ga Rabiu Biyora

Shi ya kawo kansa yana neman alfarmar a taimaka masa a rufa masa asiri kuma a shirye yake yayi tafiyar Atiku. Babu wanda ya san shi amma tunda siyasa ce na shawarci zuwansa tabbas zai taimaka. 


Daya ga ya shigo sai ya fara bada sharadi cewa sai anyi masa ihsanin da duniya zata gani tace lalle ya koma gidan arziki. Hakan kuwa akayi duniyar kuma ta gani. Dama Bulama Bukarti ka ja min kunne tun a wancan lokaci amma tunani bai je nan ba domin duk wanda ya shigo tafiyarka saboda abun duniya, idan wani ya bashi abunda yafi naka tabbas barinka zai ya tafi inda bukatarsa zata biya. 

Ga mai hankali idan ya kalli rubutunsa dana Bulama anan kasa tabbas zai gane mutum ne mai kwadayi da son abun duniya. Ka sani idan kayi haka ne don ka wulakantamu toh kanka ka wulakanta. kuma shi maci amana ya san karshensa. Sai dai ko kana so ko baka so mun zama silar arzikinka da ace ba muyi maka ba sun ji haushi da a haka zaka kare. 

Atiku bai san da kai ba ni na sa shi yayi jawabi akanka a matsayinsa na mai sauraron na kasa dashi kuma tun daga wannan lokaci shafinka ya rufe a wajensa. Don haka nasarar mu a wajen Allah muke nema ba wani kato ba. Shi ke bada mulki ga wanda yaso lokacin daya so. Da kai da babu duk dayane. 

Atiku Da Jama’arsa kazo ka ganshi. Abi duniya sannu a hankali mun saka ma da alkhairi ka saka mana da tsiya.
Maje El-Hajeej Hotoro.


No comments:

Post a Comment