Monday, 14 January 2019

Nima ina fama da yunwa>>Amaechi

Shugaban gangamin yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi ya baiwa masu cewa akwai yunwa a kasarnan amsar cewa shima fa yana fama da yunwarnan.Ya bayyana hakane a jihar Bauchi ranar Asabar din da ta gabata yayin yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Amaechi yace shima yana cikin yunwa dalilin satar kudin kasarnan da jam'iyyar PDP ta share shekaru 16 tana yi, ya kara da cewa yanzu PDP ta talaucene shiyasa take son sake samun dama dan ta sace dukiyar kasar.
Punch.

No comments:

Post a Comment