Thursday, 10 January 2019

Nyako ya roki mutanen jihar Adamawa su zabi dan sa na jam’iyyar ADC gwamnan jihar

Tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya roki mutanen jihar Adamawa su yi masa kara su zabi dansa AbdulAzeez Nyako da yake takarar zama gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar ADC.


Nyako ya bayyana cewa dansa ne AbdulAzeez zai dawo da martabar jihar da gwamna mai ci Jibirilla Bindow ya yagalgala a idanun mutane.

” Lokaci yayi da mutanen jihar za su dawo daga rakiyar gwamna mai ci wato Jibirilla Bindow, jama’a su canja shi da dana na jam’iyyar ADC. A gwada jam’iyyar ADC.

” Bindow da jam’iyyar sa APC sun ba mutanen Adamawa kunya matuka domin kuwa babu wani abin azo a gani da gwamnatin ta tabuka a shekarun da tayi ta na mulki a jihar.
PremiumtimesHausa.


No comments:

Post a Comment