Wednesday, 23 January 2019

Rahama Sadau ta dauki nauyin kai Sani Garba S.K Asibiti

Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta dauki nauyin kai abokin aikinta dake fama da rashin lafiya, Sani Garba S. K asibiti da kuma daukar nauyin duk abinda za'a yi masa magani, abokin aikin Rahamar, Aminu S. Bono ne ya bayyana haka:Ga abinda ya rubuta kamar haka:

RAHAMA SADAU CE TA DAUKI NAUYIN KAI SANI GARBA SK ASIBITI DA DUKKAN ABINDA ZA AYI MAGANI

Assalam zanyi wani takaitaccen jawabi akanki @rahamasadau 
Bama yiwa dan Adam adalci a sanda yayi kuskure muyita yayatawa Amma idan kayi alheri sai muyi gum da bakinmu 

Nasani abinda zanyi bazaki so ba saboda kinyi kokarin boye alherin da kikayi don kwadayin ladanki agun Allah,dukda haka fadar mu bazata hana Allah yabaki lada akan kyakyawar niyarki ba mun sani kuna nan dayawa a kannywood kuna kokarin taimakawa badon a sani ba sai don zatin Allah.

ALLAH YA BIYAKI DA GIDAN ALJANNA

No comments:

Post a Comment