Tuesday, 8 January 2019

RAN MAZA YA BACI, 'YAN TA'ADDA KUN SHIGA UKU: Buratai ya jagotanci sojin kundumbala yaki da Boko Haram

Shugaban sojojin Nigeria Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai mai dala'ilun yaki, ya jangoranci kaddamar da hari da kanshi akan 'yan ta'addan Boko Haram a sassan jihohin Borno da Yobe wanda aka samu nasaran hallaka 'yan ta'adda sama da dari kamar yadda rundinar sojin Nigeria ta bayyana

Wannan hoton da ake gani na Janar Buratai tsohon hoto ne kusan shekaru uku lokacin da yake ziyartar dakarun mayakan sojoji dake fagen yaki a cikin jejin Sambisa, to a halin yanzu, kuma a halin da ake ciki; da kanshi yake jagorantar sojojin kundunbala wajen kaddamar da hari akan 'yan ta'addan Boko Haram

Rundinar sojin Nigeria tace yanzu haka dakarun mayakan sojin Nigeria sun kara kaimi ta yankin tabkin chadi don ganin sun murkushe duk wani barazana na 'yan ta'adda a yankin tare da taimakon jiragen yakin sojojin saman Nigeria, kuma wannan hari na musamman da ake kaddamarwa shugaban sojoji Janar Buratai yake jagoranta da kanshi

Baba Buratai muna matukar godiya bisa ga wannan sadaukarwa da kayi garemu 'yan Nigeria domin mu tsira da rayukan mu, hakika ka cancanci yabo da godiya, muna nan muna ta hayaniya hankali kwance a gidajenmu, shi kuma yana can cikin jeji yana fafatawa da 'yan ta'adda, amma duk da haka wani katon banza sai ya buda baki yace dakarun mu wai basa yin komai

Yaa Allah Ka taimaki shugaban sojojin Nigeria tare da rundinarshi Ka tabbatar musu da nasara akan 'yan ta'adda Amin
Datti Assalafiy.


No comments:

Post a Comment