Sunday, 6 January 2019

Ronaldinho ya talauce har kotu ta hanshi fita daga kasar Brazil saboda ya kasa biyan bashi

Tsohon tauraron dan kwallon kafar kasar Brazil, Ronaldinho na fuskantar matsi saboda bashin diyyar da ake bin wani gurin tallafawa matasa da ya gina a kasar tashi wanda rahotanni suka bayyana cewa ya kasa biya.Alkalin kotun da aka kaishi kara ya kwace mai Fasfonshi na tafiye-tafiye inda ya hanashi fita daga kasar ta Brazil, a sati me zuwane dai ya kamata Ronaldinhon ya je Dubai, kasar hadaddiyar daular larabawa inda zai halarci wani taro a babban dakin taron wasanni na kasa da kasa amma ba zai samu halarta ba saboda hanashi fita daga kasar tashi ta haihuwa.

An kwace fasfon na Ronaldinho da dan uwashi, Assis Moreira kamar yanda The Sun ta ruwaito ne bisa Kasa biyan diyyar gurbata muhalli da cibiyar da dan wasan ya gina ta jawo, duk da cewa an yaba da kokarin dan kwallon na gina wannan cibiya me taimakawa matasa da talakawa amma kotun ta dage cewa sai sun biya diyyar gurbata muhalli da wannan ginin ya jawo.

Kudin dai sun kai fam miliyan 1.75 wanda rahotanni sukace Ronaldinhon ya kasa biya.

Tun a watan Nuwamba na shekarar 2018 ne alkalin ya bayar da umurnin kwace fasfon na Ronaldinho amma saboda dan wasan baya kasar, yana ta yawo a kasashen Duniya ba'a samu yin hakan ba, saida ya koma gida hutun Kirsimeti sannan aka samu aka kwace.

Alkalin da ya yanke hukuncin yace suna fama ne da mutumin da yake wasa da hankalin shari'a a idon 'yan kasar Brazil da ma Duniya baki daya.

Rahotanni dai sunce tuni har mahukunta sun kwace wasu motocin alfarma uku da kuma wani zanen ado daga wani gidan iyalan dan wasan.

Sannan kuma fam 5 kacal aka samu a cikin asusun ajiyarshi.


No comments:

Post a Comment