Friday, 4 January 2019

Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon shekarar 2018

Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon shekarar 2018 ta Globe Soccer Awards da aka yi a Dubai, karo na 5 kenan yana lashe wannan kyauta.Dan shekaru 33 ya doke wanda suka nemi wannan kyautar tare watau, Kylian Mbappe da Antoine Griezzman.

Ya kuma samu rakiyar budurwarshi da danshi wajan karbar kyautar.

No comments:

Post a Comment