Saturday, 5 January 2019

Sai da na rika cewa A'uzubillahi amma duk da haka saida nayi:Inji malamin Isilamiyar da aka kama yana lalata dalibarshi 'yar shekaru 5

Malamin makarantar Isilamiya kenan da aka kama a jihar Legas yana lalata da karamar yarinya 'yar shekaru 5, Abdulsalam Salaudenn dan shekaru 43 ya amsa laifinshi inda yace makiya ne suka sashi gaba shiyasa ya aikata wannan abu.Wani dan kasa na garine ya kaiwa masu rajin kare hakkin yara rahoton malamin a yankin Igando dake Legas, sai suka bashi shawarar cewa ya samu ya kama malamin yana aikata laifin ya daukeshi hoto dan a samu kwakkwarar hujjar kamashi saboda ana ganin girmanshi a yankin idan aka tunkareshi da maganar yana iya cewa bai aikataba.

Da wanda yayi zargin ya samu daukar hoton bidiyo sai ya kaiwa 'yansanda inda aka ganshi yana lalata da yarinyar ta dubura, an kamashi dai inda da farko yayi gaddama amma da yaga bidiyonshi yana aikata laifin sai ya fashe da kuka ya amsa cewa ya aikata, kamar yanda me magana da yawun hukumar 'yansanda na jihar Legas, CSP Chike Oti ya bayyanawa Punch.

Abdulsalam ya kuma kara da cewa a lokacin da zai yi wannan danyen aiki yayi ta cewa A'uzubillahi amma duk da haka saida shedandin yayi nasara akanshi.

Ya kara da cewa koda a can baya sai da aka taba mai wannan zargin dalilin da yasa ma kenan ya bar tsohuwar unguwarshi ya canja guri.

Hukumar 'yansanda tace nan bada dadewa ba za'a gufanar dashi gaban kuliya.

No comments:

Post a Comment