Thursday, 10 January 2019

Sakonni zamu turawa mutane: Bazan yi amfani da kudin gwamnati wajan yakin neman zabe ba>>Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai taba bari a taba asusun gwamnati ba dan daukar kudi a mishi yakin neman zabe ba.Buhari ya bayyana hakane ta hannun me magana da yawunshi, Malam Garba Shehu bayan  kammala taron majalisar koli jiya, Laraba.

Ya bayyana cewa a yi amfani da sakon wayar hannu da sauran kafafen sada zumunta dan neman kuri'un 'yan Najeriya, ni bazan fitar da kudi dan a baiwa mutane su zabemu ba, injishi.

Yace 'yan Najeriya na bukatar canji, dan haka an daina siyasar bayar da kudi ga masu zabe dan su zabi dan takara.

No comments:

Post a Comment