Thursday, 10 January 2019

Saraki ya biya ma'aikatan wata karamar hukuma bashin albashin da suke bi a Kwara

Kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki ya biya ma'aikatan karamar hukumar, Irepodun dake jihar Kwara bashin albashin miliyan 16.9 da suke bi.Shugaban karamar hukumar, Muyiwa Oladipo ya bayyana cewa, wannan cika alkawari ne domin tun a baya dama Sarakin yayi alkawarin biyan bashin da wasu ma'aikatan kananan hukumomin jihar suke bi, kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment