Sunday, 13 January 2019

SHAWARA ZUWA GA MASU IKO AKAN MAYAKAN SOJIN NIGERIA

Da farko ina mai jaddada yin jinjina da mika sakon godiya da karfafa gwiwa ga rundinar sojin Nigeria bisa kokarin da suke na tabbatar da sun share burbushin 'yan ta'addan Boko Haram daga doron duniya


Bayan haka ina so nayi amfani da wannan dama wajen yin kira ga shugabannin mayakan sojin Nigeria kan cewa su lura da wata kuskure da ake tafkawa a fagen yaki da 'yan ta'adda, Kuskuren kuwa shine duk lokacin da sojojin kundunbala suka fatattaki 'yan ta'addan Boko Haram a kan hanya ko a sansaninsu mayakan sojojin su kan kwato makaman 'yan ta'addan da kuma tutarsu

Ita wannan tuta na 'yan ta'addan Boko Haram tana dauke da kalmar shahada, kalmar da ake furtawa a shiga musulunci, idan kuma anyi imani da ita a kan shiga Aljannah kamar yadda musulunci ya karantar, malamai sunce inda za'a dauki wannan kalma misalin wacce take rubuce a jikin wannan tuta na 'yan ta'adda, sai a hada nauyin dukkan abinda yake cikin sammai bakwai da kassai bakwai a kawo wannan kalma ta shahada a auna a sikelu to sai kalmar ta rinjayi nauyin abinda yake cikin sama da 'kasa

Kalmar shahada kalmace mai tsarki, tana da Girma sosai a musulunci, sannan Allah (SWT) Ya ambaci kalmar a cikin Qur'ani gurare da dama, don haka bai kamata ayi wasa da kalmar ba a cikin kowani yanayi da mataki, balle kumar har a shimfide kalmar a kasa a daura wasu abubuwa a kai

Kamar yadda kullun muke yiwa rundinar sojin Nigeria fatan samun nasara a kan 'yan ta'adda muna rokonsu a duk lokacin da sukaci nasara akan 'yan ta'adda tare da kama tutarsu to ayi kokari wajen adana tutar indai tana dauke da kalmar shahada, muna jin tsoron kada a fusata Allah Ya hana sojojinmu samun nasara akan 'yan ta'addan Boko Haram 

Allah Ya sa a fahimceni da idon basira sannan kuma a gyara kuskuren
Ina rokon Allah Ya tabbatar da nasaran sojojin Nigeria akan 'yan ta'adda Amin.
Datti Assalafiy.


No comments:

Post a Comment