Friday, 11 January 2019

Shugaba Buhari ba zai iya fitar da Najeriya daga matsalolin da take ciki ba>>Rahoton kasar Amurka

Wata kungiya ne zaman kanta dake saka ido akan harkokin siyasar Duniya dake kasar Amurka, Eurasia ta bayyana shugaban kasa, Muhammadu Buhari a matsayin wanda ba zai iya warware matsalar da Najeriya take ciki ba saboda wasu dalilai.
A cikin rahoton karshen shekara da ta fitar,Eurasia ta bayyana shugaban kasa, Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya manyanta kuma bashi da kwarewa a harkar siyasa ga kuma rashin lafiya da ke damunshi, kamar yanda Guardian ta ruwaito.

Wadancan dalilai na sama ne Eurasia, musamman maganar rashin lafiya tace idan ta cigaba, zata hana shugaban kasar warware matsalolin da Najeriya ke ciki, ta kara da cewa shugaban bashi da kuzarin da zai iya yin aiki tukuru wajan kai Najeriya ga ci.

No comments:

Post a Comment