Wednesday, 9 January 2019

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin da yasa be canja shuwagabannin hukumomin tsaron kasarnan ba

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana dalilan da suka sa har yanzu be canja shuwagabannin hukumomin tsaron kasarnan ba inda yace ya dauki alhakin duk wasu kura kurai da suka yi.Shugaba Buhari ya bayyana hakane a wata hira da yayi da Arise TV a daren ranar Litinin din data gabata, yace a lokacin da ake tsaka da yakin 'yan ta'adda idan aka yi garajen canja shuwagabannin hukumomin tsaro da shugaban 'yansanda to za'a samu gasane a tsakanin jami'an.

Ya kara da cewa akwai da yawa daga jami'an tsaron da suke so su zama shugaban sojin kasa dana sama dana ruwa da kuma shugaban 'yansanda amma fa mutum daya ne zai samu mukamin, kuma kada a manta cewa wannan gwamnatince ta nada masu ci din na yanzu.

Ya kara da cewa duk cikin su babu wanda yawa sanin sosai da sosai kawai dai ya bi tarihin ayyukan da suka yi ne sannan ya zabi wanda yake ganin sun dace sannan ya kara da cewa, wata kila sun baiwa mutane kunya, ayyukan da suka yi basu gamsar ba amma ya dauki alhakin rashin canja su.

Da yake amsa yambayar cewa mafi yawan shuwagabannin hukumomin tsaron kasarnan 'yan Arewane, shugaba Buhari yace, a nada shuwagabannin hukumomin tsaro ya kamata shugaba ya lura sosai, musamman a gidan soja inda yayi aiki kusan shekaru 20, yace duk da yasan akwai tsarin raba mukamai daidai ga bangarorin kasarnan amma ba'a karawa mutum mukami bisa la'akari da jihar da ya fito idan aka yi haka to za'a sha mamaki.

Ya ci gaba da cewa dolene a yi amfani da biyayyar mutum, gwarewar aiki, kudirinshi na ganin an cimma burin gwamnati da kuma amsuwarshi tsakanin abokan aikinshi, shugaba Buhari ya kuma ce, jam'iyyar adawa ta PDP ba zata rasa hannu a matsalar tsaron da ake fama da ita a kasarnan ba domin sun kwashe shekaru 16 suna mulki, sun sace kudi ba kadan ba kuma zasu iya yin amfani da wannan kudin wajan ganin sun kunyata gwamnatinshi.

Akan maganar cewa ya mayar da yankin inyamurai saniyar ware kuwa, shugaba Buhari yace, kwata-kwata kuri'un da ya samu a zaben 2015 daga gaba dayan yankin Inyamurai 198,000 ne, wanda bai wuce abinda karamar hukuma daya zata bashiba amma duk da haka ya basu ministoci 4 wanda ko daya daga cikinsu be sani ba sannan jihohin Arewa 7 ya basu kananan ministoci to ta yaya za'ace ya mayar dasu saniyar ware?


No comments:

Post a Comment